Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Tarayya ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II raddi tana mai cewa, duk da ba ya tare da ita, akwai buƙatar ya ajiye son rai da nuna ɓangaranci ya mayar da hankali kan buƙatun ’yan Nijeriya, tana mai cewa, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta buƙatar sai sarkin ya tallata kyawawan manufofinta kafin ta karɓu.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, a yayin wani taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Cif Gani Fawehinmi, da ya gudana a ranar Laraba a Jihar Legas, Sarkin Kano na 16 ya furta kalaman cewa, yana da yadda zai iya tallata kyawawan manufofin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu har su kai ga karɓuwa a wajen ’yan Nijeriya, amma ba zai aikata hakan ba.
A yayin gabatar da jawabi, Sarki Sanusi II ya ce, ba zai bai wa Gwamnatin Tinubu kowacce shawara da sunan taimako ba dangane da halin da ƙasar ta tsinci kanta ta fuskar tattalin arziki.
A cewar Sarkin, zai iya yin tsokaci kan wasu batutuwa da suka shafi Nijeriya da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma shawarar yadda za a iya kaucewa hakan.
Sai dai a cewarsa, ba zai yi hakan ba, domin muddin ya bayar da wata shawara, tamkar ya taimaki gwamnatin ta Tinubu ne, kuma a halin yanzu ba shi da niyyar taimakon nata.
A cikin wata sanarwa ta mayar da martani da Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya fitar a jiya, gwamnatin ta nuna takaicinta “kan yadda matakan da take ɗauka waɗanda ƙwararru a duniya suka amince da su, ciki har da shi Sarki Sanusi II ɗin, a yanzu yake sukar su, saboda kawai ba ya tare da gwamnatin.
“Gwamnatin Tinubu ta yarda da cewa, Sanusi, da ma duk kowane ɗan Nijeriya, na da damar faɗin ra’ayinsa ta hanyar jinjina ko kuma suka kan yadda ake tafiyar da gwamnati.
“Sai dai abin mamaki ne a ce shugaba, musamman wanda ya fito daga ɓangaren da ake girmama faɗin gaskiya da adalci, zai fito fili ya nuna cewa, yana ƙin faɗin gaskiya, saboda son rai da kuma tunanin ana ƙin sa.
“Sannan kuma gwamnatin nan ba ta buƙatar amincewar Sarki Sanusi kan muhimman manufofinta, waɗanda a halin yanzu sun kai wata gaɓa da wajibi ne a ɗauki irin waɗannan tsauraran matakai da tsare-tsare domin magance matsalolin tattalin arziki, waɗanda kuma a yanzu sun fara samar da ci gaban da ake buƙata.
“Gwamnati na ɗaukar matakan da za su kawo sauyi ne ba don suna da sauƙi ba, sai dai domin suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da makoma mai kyau da kuma cigaba mai ɗorewa ga ƙasar, kamar yadda Sarki Sanusi ya yi ta fafutukar ganin an samar,” inji sanarwar.
A cewar gwamnatin, “sake gina Nijeriya na buƙatar haɗin kai, mayar da hankali da kuma sadaukarwa daga dukkanin masu ruwa da tsaki, kuma a matsayinmu na gwamnati, muna buƙatar shugabbanin al’umma su guje wa kalaman da za su kawo cikas ga amincewar da al’umma ke da shi a kanmu.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “wannan wani lokaci ne mai muhimmanci a ƙasar, kuma abin da ake buƙata shi ne haɗin gwiwa ba rarraba hankali ba.
“Gwamnatin Bola Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba kan manufofinta na kai Nijeriya ga tudun-mun-tsira, kuma ƙofarta a buɗe take, domin tattauna wa masu muhimmanci da masu ruwa da tsaki, a yayin da kuma take tsayin daka kan fifita buƙatun Nijeriya fiye da komai.”
