Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Nijeriya ta sanar da cewa za a samar da shirin tiyatar cire ɗa cikin sauƙi, CS, kyauta ga duk mata masu juna biyu da ke buƙata.
Wannan babban sauyi ya fito ne daga bakin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, a rana ta biyu na taron haɗin gwiwa na shekara-shekara (JAR).
Wannan shiri dai wani ɓangare ne na sabon shirin rage mace-macen mata masu juna biyu (MAMII), wanda ke da nufin magance yawaitar mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa a Nijeriya.
Nijeriya ce ƙasa mai yawan fama da mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a duniya, inda mata 512 ke mutuwa a cikin 100,000 masu rai yayin da jarirai 41 ke mutuwa a cikin 1,000 masu rai. Abubuwan da ke haifar da mace-macen sun haɗa da rashin muhimman ayyukan kiwon lafiya da rashin isassun kayan aikin kiwon lafiya, musamman a yankunan karkara.
Ta hanyar aikin MAMII, gwamnati na ƙoƙarin magance waɗannan ƙalubalen ta hanyar faɗaɗa hanyoyin samun ingantattun shirin kiwon lafiya, ƙarfafa tsarin kiwon lafiya a matakin farko (PHC), da ƙara shigar da al’umma cikin shirye-shiryen kula da lafiyar mata da yara.
Ana sa ran wannan shiri zai inganta sakamakon kiwon lafiyar mata masu juna biyu da kuma rage mace-macen mata.
