Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala kashi na biyu na shirin kula da lafiyar al’ummar jihar kyauta da ta faro.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, a watan Agustan da ya gabata kashin farko na shirin kula da lafiya kyautar ya kankama inda aka yi wa masu fama da lalurori daban-daban magani ba tare da sun biya ko taro ba.
Idris ya ce mutum 1,858 ne aka samu nasarar yi musu magani a tsakanin kashin farko da na biyu na shirin.
Ya ƙara da cewa, an fara kashi na biyu na shirin a ƙarshen Nuwamba, sannan aka kammala a makon farko na watan Disamban da ake ciki.
Ya ce, “Gwamna Dauda Lawal ya ƙirƙiro wannan shiri ne don magance matsalolin rashin lafiya da suka haɗa cire hakiya, ƙabar ciki, matsalar yoyon fitsari (VVF) da ilimintarws game da kula da lafiya.
“Daga cikin waɗanda aka yi wa aiki sun haɗa da mutum 747 da aka cire wa ƙari da 246 da aka cire wa tsiro da 781 aka cire wa hakiya, sai kuma mutum 84 da aka yi wa maganin yoyon fitsari (VVF).
“Shirin wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Farfesa A. I. Mungadi da sauran ƙwararrun ma’aikata, ya samu nasarar yi wa mutum 1,858.”
Sanarwar ta ce an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar shirin ne daga sassan ƙananan hukumomi 14 da jihar ke da su.
