Erling Haaland yana cikin ‘yan takarar gwarzon gasar firimiya na watan Satumba, bayan da aka buga wasan mako na bakwai a karshe mako.
Dan wasan City yana takara ne tare da Cole Palmer na Chelsea da Luis Diaz na Liverpool da Ollie Watkins na Aston villa da David Raya da Gabriel dukkansu daga Arsenal.
Haalan mai shekara 24 ya taka rawar gani a watan Satumba, wanda ya zura ƙwallo uku a raga a wasa uku a firimiya.
Ya fara da cin biyu a karawar da City ta doke Brentford 2-1 a Etihad, inda Pep Guardiola ya haɗa maki uku a karawar a farkon makon Satumba.
Haka kuma shi ne ya fara cin Arsenal a minti tara da take leda a wasan hamayya da suka tashi 2-2 ranar 14 ga watan Satumba a Etihad.
Kawo yanzu Haaland ya zura ƙwallo sama da 100 a raga, ya zama na 19 da suka yi wannan bajintar a City, bayan wasa 105 da ya buga.
Haka kuma Haaland shi ne kan gaba a Premier League a yawan cin ƙwallaye mai 10 a raga, bayan wasa bakwai da fara kakar bana.
Ranar Laraba da tsakar dare za a rufe kaɗa ƙuri’a, wato ranar 9 ga watan Oktoba, domin karrama gwarzon firimiya na watan Satumba.
