Chelsea ta karbi tayi kan ɗan wasanta mai shekara 28, Ben Chilwell, wanda sau guda ya taka mata leda a wannan kakar.
Arsenal ta tura wakilai domin sa ido kan ɗan wasan gaba a Atalanta mai shekara 25 asalin ƙasar Italiya, Mateo Retegui.
Rashin jituwa tsakanin kocin AC Milan, Paulo Fonseca da ɗan wasan Faransa mai tsaron baya, Theo Hernandez na iya sa ɗan wasan mai shekara 27 ya bar San Siro yayin da Real Madrid da Manchester United ke zawarcinsa.
Tottenham ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Atalanta da Ingila, Ben Godfrey mai shekara 26, a yarjejeniyar gajeren lokaci.
Lille na iya katse kwantiragin ɗan wasan Faransa mai shekara 31 Samuel Umtiti, wanda tun watan Janairun 2024 bai yi wasa a saoda raunin da yake samu a gwiwa.
Duk da raɗe-raɗin da ake yaɗawa, ɗan wasan Liverpool Luis Diaz, mai shekara 27, na nan zama daram a Anfield, babu wani batun sauya sheka.
Wakilin ɗan wasan gaba a Chelsea Christopher Nkunku ya gabatarwa Barcelona tayi kan ɗan wasan asalin Faransa mai shekara 22.
Kocin Manchester United Ruben Amorim daga Portugal na fuskantar matsin lamba kan ya ɗauki ɗan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford mai shekara 27, koda kuwa rashin ɗan wasan zai iya haifar da rauni a daidaita matsayarsu kan cinikin ‘yan wasa a watan Janairu.
Newcastle na iya duba tayi kan ɗan wasan Italiya mai shekara 24, Sandro Tonali a sabuwar kaka domin cimma dokokin cinikin ‘yan wasa da riba, yayin da Juventus ke nuna kwaɗayinta.
Bayern Munich na duba yiwuwar saye ɗan wasan Bundesliga a Borussia Dortmund, Jamie Gittens mai shekara 20.
Everton na shirin gabatar da sabon kwantiragi kan mai tsaron ragarta, Jordan Pickford, ɗan shekara 30 a kokarin ci gaba da riƙe shi a ƙungiyar.
Paris St-Germain na son bai wa Arsenal dama na saye ɗan wasanta na Faransa da ba ta wani yayi Randal Kolo Muani, mai shekara 26.
Chelsea da Arsenal da Tottenham sun aike wakilansu Club Brugge domin sa ido kan ɗan wasan Belgium Maɗim de Cuyper, mai shekara 24.
FC Zurich ta tuntubi Arsenal kan ɗan wasanta na Ingila mai shekara 21, Nathan Butler-Oyedeji.
An bai wa Manchester United damar saye ɗan wasan gaba daga Nijeriya Victor Osimhen a watan Janairu. Napoli na son ta cimma yarjejeniyar musaya da ɗan wasan mai shekara 25 da yanzu ke zaman aro a Galatasaray.
Kocin Brighton Inigo Calderon, mai shekara 42, ya yi nisa a tattaunawar tafiya Bristol Rovers.
Bayern Munich na da kwarin gwiwar saye kan ɗan wasan Jamus mai shekara 21, Florian Wirtz da Bayer Leverkusen ke ƙoƙarin tattaunawa da shi kan sabon kwantiragi.
Kocin Leicester City Ruud van Nistelrooy na son amfani da alaƙarsa wajen samun aikin Manchester United a watan Janairu.
Manchester United ta soma bincike kan wanda zai maye gurbin Erik ten Hag, da zarran tsohon kocinsu ya sa hannu kan sabon kwantiragi a watan Janairu.
