Moroko za ta sake karɓar baƙuncin AFCON a 2026

Spread the love

Moroko za ta sake karɓar baƙuncin kofin Afrika na Mata WAFCON karo na uku a jere a 2026, yayin da aka sanar da wasannin share fagen shiga gasar a ranar Alhamis kuma ƙasashe 38 ne za su fara fafatawa a gasar, an samu ragin ƙasashe huɗu da za su buga gasar 2024.

Kowacce ƙasa za ta buga wasa biyu, gida da waje, domin samun 11 da za su hadu da mai masaukin baƙi su buga gasar WAFCON ta 2026, sannan ƙasashe shida da ke saman jerin jadawalin Afrika da suka haɗa da Nijeriya da South Africa da Ghana da Cameroon da kuma Ibory Coast, za su samu tikitin zuwa zagaye na biyu ko da ba su fafata ba.

Za a yi wasan zagaye na farko ne a watan Fabrairun 2025, sannan a yi na biyu a watan Oktoban shekarar mai zuwa sai dai har yanzu dai hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika CAF ba ta sanar da ranar da za a fara gasar ba.

Botswana da Dr Congo da suka je matakin ƙarshe na 2024 bai zama dole su halarci gasar ta 2026, saboda koma bayan da suka fuskanta kuma za su kara da juna a wasan farko sannan wanda ya yi nasara zai fuskanci gwarzuwar gasar Afrika ta Kudu.

Gasar WAFCON ta 2024 da za a yi a Moroko aka jinkirta za a gudanar da ita ne daga ranar 5 ga watan Yuli zuwa 26 na shekara mai kamawa, saboda matsar da ita baya da aka yi saboda gasar Olympics ta 2024 da aka yi a birnin Paris.

By ukarofi