Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Southampton na daf da tabbatar da zaman dindindin na matashin ɗan gaban Senegal Nicolas Jackson, wanda Villarreal ta sa masa farashin yuro miliyan 20.

Crystal Palace na son dawo da ɗan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher ƙungiyar saboda yadda matashin na tawagar Ingila ya taka rawar-gani a lokacin da yake zaman aro a Eagles ɗin a kakar da ta wuce.

Darektan wasanni na Napoli Cristiano Giuntoli ya ce yana da kwarin gwiwa ƙungiyar za ta iya sayen matashin ɗan wasan tsakiya na Angers da Morocco Azzedine Ounahi, wanda kuma ake dangantawa da tafiya Aston Villa da Leeds United.

Wakilin ɗan bayan Belgium Yannick Carrasco ya ce ana tattaunawa kan tafiyarsa Barcelona daga Atletico Madrid, yayin da shi kuwa ɗan gaban Holland Memphis Depay, zai bar Barcelona zuwa Atletico Madrid ɗin.

Borussia Monchengladbach ta yi watsi da tayin da Bayern Munich ta gabatar mata na yuro miliyan 8 da karin Yuro miliyan 1 a kan golan Switzerland Yann Sommer, mai shekara 34.

Tsohon kociyan Leeds United Marcelo Bielsa shi ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Mexico ke son nadawa a matsayin sabon kociyan tawagar ƙasar.

Ana sa ran golan Jamus Loris Karius, ya tsawaita kwantiraginsa a Newcastle United har zuwa bayan watan Janairu, yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.

Barcelona na matuƙar son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Jamus Ilkay Gundogan a rahusa da bazara lokacin da kwantiraginsa zai kare da Manchester City.

Chelsea na jiran tsammani a kan ɗan gaban Brighton Leandro Trossard, wanda ake dangantawa da tafiya Arsenal ko Tottenham, amma kuma ana ganin abu ne mai wuya ƙungiyar tasa ta karɓi kuɗin da yake ƙasa da fam miliyan 25 a kan ɗan Belgium ɗin.

Fiorentina ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 da Leicester City ta gabatar mata a kan ɗan gabanta na Argentina Nicolas Gonzalez.

West Ham na shirin ɗauko aron ɗan bayan Ingila Harry Maguire, daga Manchester United.

Har yanzu Alejandro Garnacho bai yarda ya ƙulla sabuwar yarjejeniya da Manchester United ba, saboda wakilan ɗan ƙasar ta Argentine na son a ƙara wa ɗan gaban albashi a kan fam 20,000 da ake ba shi a mako.

Wannan ya sa Real Madrid da Juventus suke jiran tsammani a kan matashin ɗan wasan mai shekara 18 wanda kwantiraginsa zai kai har 2024, da kuma yuwuwar tsawaitawa da shekara ɗaya.

Arsenal ta tuntuɓi Bayer Leverkusen a kan ɗan gabanta Moussa Diaby amma kuma ƙungiyar ta Jamus ba ta son sayar da ɗan Faransar mai shekara 23 a watan Janairu.