
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta rage adadin matakin buƙatar karɓar bashi na masu gudanar da harkokin Hajji da Umarah daga Naira miliyan 250 zuwa miliyan N100, bayan shawarwari mai zurfi da masu ruwa da tsaki gabanin ayyukan Hajjin 2027.
Shugaban hukumar, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ne ya sanar da gyaran, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na gyare-gyaren sharuɗɗan gudanar da harkokinsu na aikin Hajjin 2027 kuma yana da nufin daidaita tsarin gudanarwa cikin inganci yayin fuskantar masu jagorantar harkokin hajji.
A cewar hukumar, matakin ya biyo bayan da Ƙungiyar Masu Gudanar da Harkokin Hajji da Umrah ta Nijeriya (AHOUN) da sauran masu ruwa da tsaki suka koka kan buƙatar miliyan N250 da fari wanda zai sanya matsin kuɗi akansu kan halin tattali.
Bayan nazari kan shawarwarin, NAHCON ta amince da mayar da buƙatar karɓar bashin bankin zuwa Naira miliyan 100.
Ambasada Yusuf ya bayyana cewa, matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da NAHCON ke yi wajen ganin ta bi tsarin jagoranci tare da jama’a da kuma damawa da masu ruwa da tsaki, yana mai cewa sun samu nasarar hakan ne sakamakon tattaunawa da haɗin-gwiwa a madadin aiwatarwa ta gaban kansu.
Ya ƙara da cewa, hukumar tana la’akari da ƙorafe-ƙorafen masu ruwa da tsaki wajen shirya wani tsari ko bin dukkan hanyoyin da za su taimaka mata wajen samun ci-gaba a harkokinta bisa la’akari da maslahar mahajjatan Nijeriya da tabbatar da walwalar masu gudanarwa da samar da lasisin sabis na Hajji.
