Hajjin Bana: Maniyyatan Binuwai sun yi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Wata mota mai ɗauke da maniyyatan Hajjin 2023 daga Jihar Binuwai ta yi hatsari.

Hatsarin ya auku ne a ranar Juma’a yayin da maniyyatan ke kan hanyarsu ta zuwa birnin tarayya, Abuja inda a nan ake sa ran za su shiga jirgi zuwa ƙasa mai tsarki.

Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Binuwai, Mustafa Ibrahim, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga Hajj Reporters.

Tare da cewa zai ba da ƙari bayani kan batun nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *