Halifan Tijjaniyya: Sunusi ya gaji Sunusi

Daga FATUHU MUSTAPHA

A makon da ya gabata ne aka yi taron shekara-shekara na mauludin tunawa da Shehu Ahmad Tijjani a Birnin Sakkwato. Taron da ya samu halartar dubban mutane da sassa daban daban na duniya, ciki kuwa har da wasu gwamnonin qasar nan, da suka haxa da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, na Zamfara Bello Matawalle, tsohon Gwamnan Jihar Imo, Mista Rochas Okorocha da sauran su. Haka kuma mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ma ya samu damar halartar taron, da kuma manyan malaman ɗariƙar daga ciki da wajen wannan ƙasa.

A yayin wannan taro dai, an kuma naxa sabon halifan ɗariƙar ta Tijjaniya, wanda zai zama kamar shi ne, wakilin Shehi Ibrahim Nyassi a Nijeriya, inda aka bayar da sanarwar naɗa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a wannan matsayi. Wannan sanarwa dai ta fito ta bakin babban muƙaddamin ɗariƙar ta Tijjaniyya Nyasiyya a Kaulaha.

Shi dai wannan matsayi an fara yin sa ne, tun a shekarar 1961, bayan da rikici ya taso tsakanin Sheikh Malam Nasiru Kabara da Sheikh Ibrahim Nyassi a Kano. A wannan lokaci Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello Sardauna, ya kafa wani kwamiti domin sasanta rikicin, inda kwamitin ya bayar da shawarar hana Sheikh Nyass zuwa Nijeriya, sai dai Sardauna ya ba shi shawarar da ya nada wakilin sa da zai ringa hulɗa da mutanen sa ta kan sa, a saboda haka ya naɗa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a matsayin halifan sa a Nijeriya. Bayan rasuwar sa ne aka naɗa Malam Isiyaku Rabiu a matsayin halifa, sai kuma Muhammadu Sunusi II a matsayin halifa a wannan zamani. To amma waye Sheikh Ibrahim Nyassi ?

An haifi Sheikh Ibrahim Ibn Sheikh Abdullah al Kaulayi al Nyassi a shekarar 1900 ya kuma rasu yana da shekara 75 a 1975. Shi ne baqar fata na farko da ya fara jan sallah a Masallacin Azhar da ke Kairo, ya samu tagomashi saboda irin gudunmawar da ya bayar wurin yaƙi da mulkin mallakar Turawan Yamma a Ƙasashen Africa. Ya tava zama mai baiwa Shugaban Ƙasar Ghana na farko, Kwame Nkrumah, ya abokanci Shugaban Qasar Misra, Gamel Abdelnasar, sannan kuma ya ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Sarkin Makka na wancan lokacin Sheikh Faisal. Shi ne ma dalilin da ya sanya suka kafa Majalisar Musulunci ta Duniya (World Muslim League) kenan, inda Sarki Faisal ya zama shugabanta, shi kuma ya zama mataimaki.

Sheikh Ibrahim ya taso a hannun mahaifin sa Sheikh Abdullahi a garin a qauyen Tayba Nassene a Ƙasar Senegal, yana saurayi mahaifin sa ya bar garin Tayba ya koma Kaulaha, Inda ya kafa zawiyyar sa mai suna Lewna Naseen. A wanna lokaci Sheikh Ibrahim ya raba rayuwar sa gida biyu, tsakanin noma da karatu a gaban mahaifin sa. Bayan rasuwar Mahaifin sa a 1922, sai ya maida himma wurin noma da karantarwa. A wannan lokaci bai amince ya nuna kan sa a matsayin halifan mahaifin sa ba, saboda ƙarancin shekaru. Sai dai kuma an fara samun takun saqa tsakanin sa da yayan sa, sheikh Muhammad Khalifa, saboda ƙanin na sa ya fara tara ɗalibai.

A shekarar 1929 ne ya sanar da almajiran sa cewa, Shehu Ahmad Tijjani ya naɗa shi ya zama Gausu a Ɗariƙar Tijjaniya, wanda shi ne abinda ya ƙara rura wutar gaba a tsakanin sa da yayan na sa. A shekarar 1930 bayan an idar da sallar ƙaramar sallah ne, wani rikici ya varke a tsakanin mabiyan sa da mabiyan yayan na sa. Wannan rikicin shi ya sanya ya bar Kaulaha ya koma wai ɗan ƙauye da ke kusa da Kaulaha maisuna, Baay.

Anan ya fara kafa zawiyyar sa, kuma anan ne ya tara mafi yawan ɗaliban sa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya samu karɓuwa, kusan dukkan almajiran mahaifin sa suka komo suka bi shi. A kuma wannan lokaci ne, wasu larabawa daga Mauritaniya suka zo suka jaddada mubayi’ar su gare shi. A shekarar 1937 ya haɗu da Sarkin Kano Bayero a Makka, kuma anan ne ya yi masa mubayi’a ya fice daga Ɗariƙar Ƙadiriyya ya koma Tijjaniyya.

Akwai masu ganin cewa, akwai hannun turawa a wannan haɗuwa ta Sarkin Kano Bayero da Sheikh Nyass, musamman ma in aka yi la’akari da dagar da suke sha tsakanin su da mabiya Ɗariƙar Tijjaniyya Futiyya wacce ta sanya tilas aka naɗa D’o a Daɗayyawa ta Ƙasar Haɗeja, wanda nan ne hedikwatar mabiya Sheikh Umar al Futi.

Zuwan sa Kano ya ƙara faɗaɗa ƙarfin yawan mabiyan sa a Nijeriya. Ana zaton zuwan na sa, ya yi tasiri ta hanyar kashe kaifin adawa da mulkin turawa da yan Tijjaniya Futiyya ke nunawa, sannan kuma ya samarwa da Ƙadiriyya kishiya mai ƙarfi. Cikin manyan almajiran sa a Kano sun haɗa da Ciroman Kano Muhammadu Sunusi (Sarkin Kano 1953 – 1963), Walin Kano Sulaimanu, Malam Umaru na Wali, Alhaji Uba Waru, Malam Rabiu ɗan Tinki (mahaifin malam Isiyaku Rabiu), Alhaji Uba Ringim da sauran su.

Babban abinda yafi ɗaukar hankali a zuwan Shehi Nyass kamar rikicin Ƙabalu da Sadalu da ya rincaɓe a Kano a tsakanin malamai. A yayin da shi Shehu Nyass ya dage akan bawani hadisi da ya taɓa nuna Manzon Allah (saw) ya taɓa yin Sadalu, shi kuma malam Nasiru Kabara ya tabbatar da cewa Imam Maliku ya karhanta yin ta a Sallar Farilla. Wannan rikici dai ya cigaba har zuwa shekarar da ɓangaren su Malam Nasiru suka yi nasara, inda Gwamnatin Jihar Arewa ta yi masa iyaka da zuwa Nijeriya.

Ana ganin wannan mataki na ɗaya daga cikin abinda ya haddasa rikicin Sarkin Kano Sunusi I da Sardauna. A wannan lokaci ne ya naɗa Sarkin Kano Sunusi I a matsayin halifan sa, ya kuma umarci dukkan mabiyan sa da masu son kai masa ziyara da su koma wurin Sarki Murabus. Ya cigaba da riƙe wannan muqami har bayan ya ajiye rawanin sa, har lokacin da Allah ya yi masa rasuwa.
Rikicin halifanci bai ƙare ba, har a lokacin da aka naɗa Malam Isyaka Rabiu a matsayin halifa.

A wannan lokaci wasu manyan Malaman Tijjaniyya sun ƙi amincewa da wannan halifanci na sa, musamman Sheikh Ɗahiru Bauchi. Wannan rikici shi ya haifar da saɓanin da ke cikin ɗariƙar a yau, a yayin da vangaren Ɗahiru Bauchi ke kallon ɓangaren Malam Isyaka a matsayin waɗanda karatun su bai kai a ba su wannan muƙami ba. A dalilin haka ne ma, a Shekarar 2019 aka samu rabuwar kai da har ta kai wani ɓangaren ya yi Mauludin sa na shekara a Kaduna, ɗayan kuma ya yi a Abuja.

To amma duk da wannan naɗi da aka yi, a yanzu haka wani sabon rikicin ya ƙara kunno kai, inda wasu ke adawa da wannan naɗi da aka yi wa Sarki Sunusi II. Ana zargin dai akwai hannun wasu manyan ‘yan siyasa da ke da banbancin ra’ayi da Sarki Sunusi I, musamman ɓangaren Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje. Wasu na kusa da Sarkin da na zanta da su sun tabbatar min da cewa, da niyya aka juya zancen domin a yi wa Sarkin bi ta da ƙulli, dukan kabarin kishiya. Har ma sun yi zargin cewa an baiwa wasu manyan malamai na Tijjaniyya kuɗi domin su nuna ƙin goyon bayan su ga wannan naɗi.

A yanzu haka dai babban ƙalubalen da ke gaban sabon halifan shi ne na, yadda zai ƙinke ɓarakar da ke cikin ɗariƙar, sannan kuma yadda zai shawo kan wasu mabiya ɗariƙar da ke wuce makaɗi da rawa wurin yabon Shehi Ibrahim Nyass. Akwai kuma batun haɗin kan musulmi da a kullum ke ƙara taɓarɓarewa, musamman ma da yake ana ganin halifan na da kyakkyawar alaƙa da mabiya Ɗariƙar Wahabiyawa dake Nijeriya.