Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka

Daga IBRAHIM YAYA

Alkaluma na tabbatar da cewa, sama da mutane miliyan shida ne suka mutu ya zuwa yanzu, tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19, yau shekaru biyu da suka gabata. Darasin da masana lafiya da jami’an ƙasa da ƙasa ke cewa, ya zama tilas a mayar da hankali a kai.

Sai dai yayin da wasu ƙasashen duniya, kamar ƙasar Sin suka yi nasarar aiwatar da managartan matakan daƙile yaduwar annobar, baya ga taimaka ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kayayyakin yaki da cutar a lokuta daban-daban, a hannu guda kuma wasu ƙasashe irin su Amurka, na neman siyasantar da batun annobar, lamarin da ya haddasa hasarar rayukan mutane masu tarin yawa. Kuma har yanzu tula ba ta rabu da kalaye ba.
Hanya guda kamar yadda mahukuntan ƙasar Sin ke kira a koda yaushe wajen ganin an yaƙi wannan annoba da ma kalubalolin dake addabar duniya, ita ce cudanyar sassan ƙasa da ƙasa.

Sanin kowa ne cewa, abu mafi muhimmanci shi ne mayar da jama’a da ma al’umma baki ɗaya a gaban komai. Kuma shi ne matakin da zai daidaita alkiblarmu a dukkan fannoni. Yanzu dai duniya na buƙatar cuɗanyar dukkan ɓangarori fiye da kowane lokaci.

Buga da ƙari, bayan wucewar annobar COVID-19, ya zama tilas ƙasashen duniya su ƙarfafa haɗin gwiwa, ƙarƙashin laimar MDD, su martaba juna, da amincewa da juna da gaskata juna, su nuna fata na gari, da haɗin gwiwa don cimma moriya tare, su kuma yi aiki tare don amfanin gaba. Saboda tuwon gobe ake wanke tukunya. Kuma malam Bahaushe na cewa, Hannu daya ba ya ɗaukar jinka.