Har yanzu ba mu ɗauki matsaya kan ƙudurin harajin Tinubu ba – Kakakin Majalisa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban majalisar wakilan Nijeriya, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta ɗauki matsaya ba a kan sabon ƙudirin haraji na gwamnatin Tinubu.

Ya bayyana hakan ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na buɗe tattauna kan sabon ƙudirin harajin a zauren majalisar da ke Abuja a ranar Litinin.

Sai dai kamar yadda jaridar Manhaja ta ruwaito, ya ce majalisar za ta yi aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na tantancewa duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara inda ya zama wajibi.

A watan da ya gabata ne fadar shugaban ƙasar ta aika wa majalisun dokokin ƙasar ƙudurorin, amma kuma majalisar zartarwa ta bayar da shawarar janye ƙudurorin saboda wasu taƙaddamomi da suke ɗauke da su.

To amma kuma Shugaba Bola Tinubu ya ƙi janyewa yana mai cewa duk waɗanda suke son bayar da gudummawarsu a kan ƙudurin za su iya yin hakan a lokacin zaman sauraron ra’ayin jama’a a majalisar.

By ukarofi