Har yanzu Igboho na hannun hukuma a Kwatano

Daga AISHA ASAS

Saɓanin rahotannin da suka karaɗe sassa kan cewa an saki jagoran gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho wai har ya keta hazo zuwa ƙasar Jamus, bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna wannan ba gaskiya ba ne, saboda ya zuwa haɗa wannan labari Igboho na can tsare a hannun jami’an tsaro a Kwatano.

Farfesa Wale Adeniran wanda shugaba ne na wata ƙungiyar Yarabawa, shi ne ya ta babbatar da cewa har yanzu Igboho na hannun hukuma a ƙasar Benin yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a dandalin zoom wanda kamfanin Heritage Multimedia TV ya shirya a Talatar da ta gabata.

Yayin shirin nasu, Farfesan ya ce, “Na yi magana da lauyansa. Lauyan ya ce ya ziyarci inda ake tsare da shi (Igboho) amma ba a bari sun gana ba. Sai dai sun tabbatar masa cewa yana nan tsare.

“Na tambaye shi ina fata ba za su ɗauki wani matakin ɓoye a kansa ba ko, sai lauyan ya ce mini hakan ba zai yiwu ba saboda sun shigar da takardar buƙatar a miƙo shi wanda kuma ana kan ci gaba da shirin hakan.”

Lauyan ya shaida wa Farfesan cewa shi da hannunsa ya kula da komai wajen shigar da takardar tare da lauyan Hukumar Kula da Shige da Fice na Benin inda ya ba shi tabbacin cewa tun da har aka shigar da wannan takarda, ba za su iya yi masa komai ba.

Adeniran ya nuna takaicinsa kan yadda mutane kan dage wajen yaɗa labaran ƙarya waɗanda ba su da tushe balle makama, labaran da a cewarsa ka iya jefa rayuwar Igboho cikin wani mawuyacin hali.

Ya ce ganin labarin ƙaryar da aka yaɗa dangane da sakin Igboho ya sanya lauyoyin ƙasa da ƙasa da ke kula da batun Igboho suka kira shi don jin gaskiyar lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *