Haraji: Gwamnatin Kaduna ta rufe wasu fitattun kamfanoni

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe harabar wasu fitattun kamfanoni a Kaduna bisa ƙin biyan haraji.

Harabar kamfanonin sun haɗa da Bankin Unity, gidan abinci na Chicken Republic da Bankin Noma (BOA) da Bankin Monument Bank (FCMB) da First City Monument Bank (FCMB) da ke kan titin Yakubu Gowon kan ƙin biyan harajin sama na Naira Biliyan 100. Hukumar ta kuma rufe fitaccen otel ɗin Hamdala.

Yayin da ta ke jagorantar kwamitin aiwatar da dokar, Sakatariyar Hukumar kuma Babbar Daraktar Kula da Harkokin Shari’a, Barista Aisha Ahmad, ta ce, hukumar ta fara aiwatar da dokar hana biyan haraji na amfani da filaye ne bayan ta gama da duk wata hanyar da doka ta tanada.