Haramta Tiwita, Gwamnati ta bada odar hukunta duk wanda aka kama da laifin take doka

Daga AISHA ASAS

Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Justice Abubakar Malami, SAN ya bada umarnin zartar da hukunci cikin gaggawa a kan duk wanɗanda aka samu da laifin take dokar haramta Tiwita a Nijeriya.

Umarnin ministan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar ta hannun hadimin ministan kan sha’anin hulɗa da jama’a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, “Malami ya bai wa Daraktan Sashen Gabatar da Ƙararraki (DPPF) na ofishinsa, da ya dukufa aiki tare da shirye-shiryen gurfanar da duk waɗanda aka samu sun yi wa dokar Gwamnatin Taryya na dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya karan tsaye.


“Malami ya buƙaci DPPF da ya haɗa kai da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet da Ma’aikatar Kula da Harkokin Sadarwa (NCC) da sauran hukumomin da lamarin ya shafa wajen tabbatar da an hukunta masu laifi ba tare da ɓata lokaci ba.”

A Juma’ar da ta gabata Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar haramta harkokin Tiwita a faɗin Nijeriya.