Labari da ɗuminsa: Kamfanonin sadarwa a Nijeriya sun soma daƙile hanyoyin shiga Tiwita

Da alama dai matakin dakatar da harkokin Tiwita a Nijeriya da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a Juma’ar da ta gabata ya soma aiki.

Domin kuwa ‘yan Nijeriya sun wayi gari Asabar sun kasa samun zarafin yin mu’amala da shafukan Tiwita kamar yadda suka saba sakamakon kamfanonin sadarwa a ƙasar, da suka haɗa da MTN, Airtel, Glo da kuma 9Mobile, sun soma daƙile hanyar shiga masarrafin Tiwita.

Kodayake dai kamfanonin sadarwar ƙarƙashin ƙungiyarsu, sun fito sun bayyana cewa sun soma daƙile hanyar shiga Tiwita ga masu amfani da layukansu kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da suka bayar a ranar Asabar.