Hare-haren ta’addanci na raguwa a Katsina lokacin Tinubu – Wazirin Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wazirin Katsina, Ibrahim Idah, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindinga sun ragu matuƙa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman a Jihar Katsina.

Wazirin Katsina ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wurin taron haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin Arewa, Idah ya ce Tinubu ya cika alƙawarin yaƙi da bazuwar makamai, wanda hakan ke haifar da raguwar hare-hare idan aka kwatanta da shekarun baya kamar yadda jaridar Premium Times ta sanar.

Ya kuma buƙaci a ƙarfafi rundunar tsaron sa-kai da makamai masu ƙarfi domin ƙarfafa tsaro, sai dai shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ja kunne kan haɗarin hakan, yana mai ba da misalin wani kwamandan sa-kai a Borno da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da zuwa ofishin hukumar da mayaƙa fiye da 50.

By ukarofi