Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwanan baya ne gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da mai da wasu ƙananan asibitocin zuwa manya asibitoci a jihar.
Asibitin garin Mai’adua na ƙaramar hukumar Mai’adua na ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗaga darajar su zuwa babban asibiti.
Kan haka al’ummar yankin suka miƙa godiyar su ga gwamna Dikko Raɗɗa bisa wannan abin alheri da yayi masu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, tsohon kakakin majalisar dokoki RT Hon Ya’u Gwajo Gwaji ya bayyana wannan matakin da gwamnan ya ɗauka, “ya nuna irin damuwarsa da ƙudirin sa na inganta harkokin kiwon lafiya ga al’ummar jihar, musamman ma mazauna yankunan karkara.
Ya bayyana cewa, maida asibitin zuwa babban asibitin zai taimaka wajen inganta lafiyar al’ummar ƙaramar hukumar har da maƙwabta.
Hon. Gwajo-Gwajo wanda ya ke riƙe da muƙamin mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Mai’adua ya kuma nuna godiya ga majalisar zartarwa ta Jihar Katsina bisa yadda ta amince da wannan ƙudiri da nufin inganta harkar lafiya a ƙaramar hukumar.
Ya ce, wannan mataki na Gwamna Raɗɗa da majalisar zartarwa ya nuna cewa gwamnatin Katsina na ɗaukar lafiyar jama’a da muhimmanci, kuma suna godiya da wannan kulawa.
Ya buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’o’i na fatan alheri da nasara ga gwamnatin Dikko Raɗɗa, domin samun nasarar aiwatar da ayyuka na alheri cikin nasara a faɗin jihar.
