Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar zartarwa ta Jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da ayyukan raya ƙasa na sama da Biliyan N23.8 a fannin lafiya, tsaro, hanyoyi, da otel-otel.
Majalisar ta amince da ɗaukaka matsayin cibiyar kiwon lafiya ta Mai’adua a Ƙaramar hukumar Mai’adua zuwa babban asibiti (General Hospital) a kan kuɗi Naira biliyan 1.3.
Kwamishinan ayyuka da gidaje, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Malam Farouk Lawal Joɓe wanda gwamna Dikko Raɗɗa ya halarta ta yanan Gizo.
Haka kuma kwamishinan ya ce, majalisar zartarwa ta amince da kashe Naira miliyan 703 domin sake gina da ɗaukaka katangar shinge da samar da shingayen tsaro a manyan asibitoci 14 . Waɗannan asibitoci sun haɗa da na Ƙanƙara, Ƙafur, Malumfashi, Ɗandume, Musawa, Faskari, Jibia, Batsari, Funtua, Dutsinma, Kurfi, Ɗanmusa, Katsina , da asibitin gwamnati na Amadi Rimi.
Kwamishina Ingawa ya bayyana cewa, “Waɗannan ayyuka wani ɓangare ne na cikakken shirin gwamnatocin mu na ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya a yankunan da ke fama da rashin zaman lafiya tare da tabbatar da samar da tsaro ga ma’aikata da marasa lafiya.”inji Injiniya Ingawa
Majalisar ta kuma amince da kashe Naira biliyan 18.5 domin gina babbar hanyar Rafin Iya–Tashar Bawa zuwa Sabuwa,inji kwamishinan.
Ta bayyana mahimmancin samar da hanyar da a cewar sa za ta inganta ayyukan tsaro, inganta zirga-zirgar kayan noma, da kuma sauƙaƙa kasuwanci da harkokin tattalin arziki a cikin yankin.
A nasa jawabin, Kwamishinan kasa da tsare-tsare na jiki, Dr. Faisal Kaita, ya sanar da amincewar majalisar kan wata yarjejeniyar ƙawance tsakanin gwamnatin Jihar Katsina da kamfanin Omo Resort don sake gina Otel ɗin Katsina.
A cewar sa yarjejeniyar da aka cimma na Naira biliyan 2.626 ya haɗa da Naira miliyan 600 na kuɗin haya na tsawon shekaru 10, Naira biliyan 2 don cikakken gyaran otel din, da kuma biyan bashin da ake bin otel ɗin.
Dangane da tsaro kuwa, majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 747,345,026.19 domin gina sabuwar cibiyar tuntuɓa ta tsaro a Katsina. Kwamishinan yaɗa labarai, Dr. Bala Salisu Zango, ya bayyana cewa wannan cibiya za ta zama na dindindin da gudanar da hidimar da ya shafi harkar tsaro.
Bayan kammalawa, za a miƙa ginin ga gwamnatin tarayya don amfani da ita a matsayin cibiyar haɗin gwiwa ga duk masu ruwa da tsaki kan tsaro a jihar Katsina,”inji Dr Bala Zango.
Dukkan ayyukan da aka amince da su sun yi daidai da babban shirin raya ƙasa na Gwamna Raɗɗa mai taken “Gina Makomarku,” wanda ya jaddada gwamnati mai haɗe da kowa, bunƙasa ababen more rayuwa masu ɗorewa a jihar, inji kwamishinan.
