Harin Israel a Ramallah ya raunana ɗaruruwan jama’a

Spread the love

Rundunar sojin Israel ta kai hari a Ramallah, inda aka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye, harsasai da kuma bindigogi a yayin far wa wata kasuwa da ake zargin na da alaƙa da Hamas. Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 58 sun jikkata, ciki har da yara da mata, inda aƙalla 8 suka ji rauni da harsasai.

Bayan tashin hankali, an kama mutane 5 da aka zarga da alaƙa da Hamas. Shaidu sun ce wannan hari ya jefa mutanen gari cikin tsoro, tare da ƙara raunana gwamnatin hukumar Falasɗinu wacce ke da hedikwata a Ramallah.

ƙungiyar Baitulmukadas ta bayyana wannan a matsayin keta dokar ƙasa da ƙasa, yayin da gwamnatin Isra’ila ta ce tana ɗaukar matakan tsaro ne kawai.

By ukarofi