Harin Kaduna: Tinubu ya bada umarnin gaggauta gudanar da bincike

*Adadin waɗanda suka rasu ya ƙaru

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada odar gudanar da cikakken bincike kan harin da jirgin sojin Nijeriya mara matuƙi ya kai Jihar Kaduna inda ya kashe gomman farar hula.

Tinubu ya kuma jajanta wa ‘yan uwa da Gwamnatin Jihar Kaduna game da waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata a harin wanda ya auku a Tudun Biri cikin yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar da safiyar ranar Talata.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana harin da abin takaici da damuwa, tare da nuna alhininsa dangane da babban rashin da iftila’in ya haifar wa Nijeriya.

Shugaban Ƙasar ya kuma yi addau’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu a harin.

Hukumomi sun ce kawo yanzu adadin waɗanda suka mutu a harin ya ƙaru daga 31 zuwa adadin da ba a bayyana ba.

Tuni dai Rundunar Sojojin Nijeriya ta ɗauki alhakin kai harin, inda ta bada haƙuri tare da cewa, hakan ya faru sakamakon bibiyar ‘yan ta’adda da take yi a yankin.

Harin ya auku ne ranar Lahadi da daddare a kansu jama’a da ke taron maulidi a yankin.