Shugaban Ukraine ɓolodymyr Zelenskyy ya bayyana cewar sabon harin da Rasha ta kai kan kwalejin horas da sojin ƙasar lokacin da ake tsaka da gudanar da wani taro ya hallaka mutane 41 tare da jikkata sama da mutum 180, galibinsu ɗaliban ƙwalejin.
Da sanyin Safiyar ranar Litinin ne, Rasha ta ƙaddamar da harin da wasu makamai masu linzami guda biyu wanda ya shafi gine-ginen asibiti da na kwalejin horar da Sojoji a birnin Poltaɓa mai tazarar kilomita 300 daga birnin Kyiɓ fadar gwamnatin Ukraine, yankin da ke ɗauke da mutane aƙalla 300,000.
Tuni dai wannan hari na Rasha ya haddasa kakkausar suka ga gwamnatin Ukraine daga ƴan ƙasar a shafukan sada zumunta, bayanda suka ɗora alhakin asarar rayukan ɗaliban Sojin kan mahukunta waɗanda suka sahale gudanar da taron duk da barazanar hare-haren Rasha a yankin.
Shugaba Zelensky a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta bayan faruwar harin, ya sanar da bayar da umurnin gudanar da binciken gaggawa kan yadda harin ya faru dama sakacin da ya kai ga asarar rayukan.
A cewar shugaba Zelensky fiye da mutane 180 ne suka jikkata a farmakin na Rasha, abin takaici har da mutane 41 da harin ya kashe bayan ya rusa babban gini a kwalejin horas da Sojojin.
