Mataimakiyar shugaban Amurka Joe Biden Kamala Harris na gab da zama halastaciyyar ƴar takarar jam’iyyar Democrats, bayan da ta sami isasshen goyon bayan da take buƙata don samun wannan tikiti.
Shugaba Biden ya ɗaga hannun Harris tare da ayyana goyon bayan sa a gareta, to sai dai hakan ba zata tabbata ba har sai ta sami wani adadi na yawan wakilan jam’iyya da zasu goya mata baya.
Idan har hakan ta tabbata, Harris zata tsayawa jam’iyyarta takara a zaɓe mai zuwa, inda kuma zata kara da Donald Trump.
Da take bayani, Kamala Haris ta ce, tana mai matuƙar farin cikin sanar da magoya bayan jam’iyyarta cewa ta sami adadin yawan wakilan jam’iyyar da take buƙatar su goya mata baya, yanzu abinda ya rage kawai shine jam’iyyar ta ayyanata a matsayin ƴar takara a hukumance.
Shima a nasa ɓangaren babban daraktan jam’iyyar ta Democrats Rust Belt Rising ya ce yana da yaƙinin cewa Harris na da kimar da zata sake ribato matasan da suka tattare komatsansu suka koma goyon bayan Trump saboda zargin cewa Biden ba zai yi nasara a zaɓe mai zuwa ba.
Jama’ar ƙasar da ma ƴan Jam’iyyar ta Democrats ne suka riƙa kiraye-kirayen Joe Biden ya janye daga takarar da yake yi, a sakamakon rashin lafiya, tsufa da kuma gigita da ke samunsa lokuta zuwa lokuta.
