
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane 20 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wasu motoci suka yi kiciɓis a yankin Hawan-Kibo da ke kan hanyar zuwa Jos a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato. Al’amarin ya faru ne a daren Juma’a wayewar Asabar, wanda ya haɗa wata tirela da bos ƙirar Hummer da ke ɗauke da wasu mutane, wasu motoci da babur guda.
An ce burki ne ya ƙwace wa tirelar a lokacin da iftila’in ke shirin faruwa, wanda ya sa ta haye kan wasu motoci da ke kan hanyar tafiya Jos, lamarin da ya haifar da motar bos ɗin ta kama da wuta. A nan ne fasinjoji 18 da ke cikinta suka rasa rayukansu, da kuma wasu mutum biyu da ke kan babur a wajen da abin ya faru.
Da yake tabbatar da faruwar al’amarin a wata hirar kiran waya da gidan talabijin na Channels, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) a jihar, Adelaja Ogungbemi, ya ce hatsarin ya auku ne a sanadiyyar tsinkewar burki daga ɓangaren tirelar. Ya ce, sun tura jami’ai wajen da abin ya faru domin buɗe hanyar da kuma kwashe mutanen da iftila’in ya rutsa da su da kai su zuwa asibitoci.
Kwamandan ya kuma kirayi direbobi da su riƙa fifita kulawa da ababen hawansu musamman gabanin fara tafiye-tafiye tare da kauce wa gudu sama da kima yayin da suke tuƙi, yana mai cewa duba halinsu akai-akai na taimakawa wajen kare faruwar haɗurra a hanyoyin Nijeriya.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar ko rundunar ‘yan sanda ba su fitar da sanarwa kan al’amarin ba.

