Hawan Sallah: Lauyoyi sun zargi Gwamnatin Tarayya da yunƙurin tozarta Sarki Sanusi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata tawagar lauyoyin kare haƙƙin ɗan-adam a Kano, ta zargi Gwamnatin Tarayya da shirya maƙarƙashiyar siyasa akan Sarki Muhammadu Sanusi na II, wanda hakan ya sa aka soke bukukuwan Sallah da masarautun Kano ke yi a kowace shekara.

A wata takardar ƙorafi da aka shigar wa ofishin Kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar, Ƙungiyar Lauyoyi ƴan Kano, ta yi zargin sanar da barazanar tsaro da Hukumar ƴan sanda ta yi da nufin hujjar hana bukukuwan a matsayin yunƙurin rage kimar Sarkin a idon al’umma.

A yayin ganawa da manema labarai, Shugaban tawagar lauyoyin, Barista Usman Imam Tudun Wazirci, ya ce hana bukukuwan ba abu ne da ya zama wajibi ba, ya na mai cewa hujjar da aka fake da ita ba ta da ƙarfi, saboda an bari a yi a Jihohin Borno, Katsina da Zamfara, warwaren da suka yi wa Kano fintinkau a barazanar tsaro.

Lauyoyin sun kuma zargi mutane marasa kishi da ƴan siyasa wajen tsoratar da al’umma da hana bukukuwan saboda adawa da dawowar Sarki Sanusi Masarautar.

Haka kuma sun ce, yin hakan ya saɓa wa dokokin ƴancin al’adu da wasu ƴanci da kundin dokar ƙasa ta bayar.

Kazalika, sun yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da Majalisar Tarayyar Turai da Majalisar Afrika da su tsoma baki kan al’amarin, wanda suka ayyana a matsayin ƙoƙarin tsangwama ga al’adu da sarautar Kano.

By Babaji