Ɗan Iyan Jarma ya yaba wa hukumar zakka da waƙafi ta Sakkwato

Spread the love

Daga WAKILINMU

An yabawa hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Sakkwato bisa yadda ta sauke nauyin amanar da Alhaji Murtala Abdulƙadir Ɗan Iyan Jarma ya ɗora mata na rabon sadaka kayan abinci da kuɗaɗe
a dukkan gundumomin jihar 87.

Alhaji Murtala Abdulƙadir Ɗan Iyan Alhaji Musa Umar Sharu, shi ya yi wannan yabon tare da jinjina ga
Shugaban hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato, da sauran muƙarrabansa, musamman ýan Kwamitin da aka ɗora wa alhakin jagorantar wannan aiki na alheri, ta bakin wakilinsa.

Ya kuma yi alƙawarin amfani da dukiyarsa wajen gudanar da ayyukan jin ƙai ga al’umma, da nan gaba za su biyo ba. Ya ce, “Babu shakka Sadaukin Sakkwato da hukumarsa sun cancanci yabo sosai, saboda yadda suka nuna gaskiya da adalci a rabon da aka gudanar a illahirin ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato 23.”

Kwamitin ya raba tallafin kayan abinci da kuɗaɗe ne a gidajen gyaran hali, masu lalura ta musamman, waɗanda suka koma addinin Musulunci, asibitoci, matan da suka rasa mazajen su, da wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci.

A jawabinsa, Shugaban hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yi godiya ga Allah tare da addu’a da fatan alheri ga wannan bawan Allah da ya ba da gudunmawar, Alhaji Murtala Abdulƙadir, bisa amincewar da ya nuna wa hukumar don ta jagoranci rabon kayan sadakar da ya bayar.

Sadaukin na Sakkwato bai manta da yabawa Gwamnatin Jihar Sakkwato ba bisa hidimomin da aka yi wa marayu da mabuƙata ta hannun hukumar da sauran waurare. Harwayau, ya yabawa Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Sanata Wamakko akan ƙarfafa su da suke yi ga ayyukan alheri na tausaya wa jama’a da ake yi.

Shugaban ya yi kira ga al’umma da su bayar da na su ɗaukin don isar da shi ga bayin Allah da ke cikin wani hali na na neman taimako.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi, sun gabatar da addu’o’i na musamman ga wanda ya bada tallafin da roƙon Allah ya biya masa dukkan buƙatun sa na alheri, ya kuma saka masa da alheri tare da maigidansa Jarman Daular Usmaniyya Dr Ummarun Kwabo da roƙon shi ma Allah ya bashi lafiya.

By ukarofi