Hedikwatar tsaro ta ƙaryata rahoton batakashi da ƴan ta’adda

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hedikwatar tsaro ta musanta rahotannin da ke cewa wasu ‘yan ta’adda daga ISWAP/Boko Haram da ke kan babura da manyan motoci ɗauke da bindigogi sun kai hari kan dakarun soji a ƙauyen Sabon Gari, ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kai harin ne domin ramuwar gayya bisa kisan kwamandansu da wasu ‘yan ƙungiyarsu da sojoji suka yi kwanan nan. Sai dai dakarun sojin sun samu nasarar daƙile harin yayin da suke dawowa daga sintiri.

An kuma bayyana cewa tawagar taimakon gaggawa ta haɗa da mambobin ƙungiyar tsaro ta farar hula (CJTF), masu sa kai, da sauran dakarun haɗin gwiwa, waɗanda suka isa wurin cikin gaggawa domin yin galaba a kan ‘yan ta’addan. Duk da haka, tawagar taimakon ta gamu da wani nakiya mai fashewa wanda ya ji wa kwamandan ‘yan sa kai rauni.

Haka kuma, dakarun sama na Operation HAƊIN KAI sun kai hari ta sama kan ‘yan ta’addan da suka tsere, inda aka tabbatar da kashe da dama daga cikinsu tare da ƙwace makamai masu yawa.

A cewar sanarwar, an kashe ‘yan ta’adda 34 tare da ƙwato bindigogi AK-47 guda 23 da harsasai sama da 200. Amma, abin takaici, an rasa rayukan sojoji shida a fafatawar. Rundunar Sojin Nijeriya ta jaddada jajircewarta wajen kawo ƙarshen ta’addanci da ‘yan ta’adda a ƙasar, tare da tabbatar wa al’umma cewa tana nan a kan matsayinta na kare lafiya da tsaron ‘yan ƙasa.

By ukarofi