Daga USMAN KAROFI
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas ta kama wata malamar makaranta mai suna Stella Nwadigo kan zargin dukan wani yaro mai shekaru uku, Abayomi Michael, a makarantar Christ-Mitots dake Ikorodu.
Nwadigo ta shiga hannun hukuma bayan wani bidiyo ya bayyana a intanet, inda aka nuna tana azabtar da yaron. Bidiyon ya yaɗu sosai a kafafen sada zumunta, inda mutane suka nuna ɓacin ransu tare da kira ga hukuma ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Legas, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamen a ranar Laraba. Ya ce, “An kama malamar kuma tana tsare yanzu haka ana gudanar da bincike a kanta. Za a ɗauki matakan da suka dace don ganin an tabbatar da adalci.”
