Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya, DSS, ta musanta kai samame ofishin hedikwatar ƙungiyar ƙwadago ta NLC.
A ranar Laraba da daddare ne dai wasu jami’an tsaro ɗauke da manyan makamai suka kai samame ofishin ƙungiyar, tare da yin waon gaba da wasu takardu.
ƙungiyar ta NLC ta zargi jami’an tsaron farin kaya na DSS ta ƙaddamnar da samamen.
ƙungiyar ta ce, jami’an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin ƙarfe 8:30
To sai dai cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukanta na sada zumunta ta musanta zargin
“Muna so kowa ya sani cewa jami’an DSS ba su kai kowane irin samame kan ofishin NLC da ke Abuja ba”, inji sanarwar
