Daga AISHA ASAS
Hukumar Tace Finafinai ta Najeriya (NFVCB) tare da haɗin gwiwa da Babban Taron Finafinai da Sinema na Legas (LIFACC) suna farin cikin sanar da taron Baji Kolin Masu Shirya Finafinai na Najeriya da kuma Babban Majalisar Gudanarwar Sinema. Wannan taro dai an shirya shi ne domin ya zama wani gagarumin biki ga duk masu ruwa da tsaki a harkar finafinan Najeriya.
Dokta Shaibu Husseini, Babban Darakta kuma Babban Jami’in NFƁCB, ya miƙa gayyatar ga dukkan masu ruwa da tsaki a masana’antu da suka jiɓinci sha’anin fim, inda yake fatan su halarci taron. Taron NFƁCB a cikin LIFACC 2024 na nufin samar da bayanai masu muhimmanci dangane da sabbin abubuwa da ƙa’idodi da suka shafi yin skit, bidiyon kiɗa, rarraba finafinai, kashe-kashensu, da kuma makomar masana’antar finafinai a Najeriya.
Mista Theo Akatugba, wanda ya kasance jagaba, kuma ma’asassi, babban darakta na LIFACC, ya bayyana farin cikinsa ga taron mai zuwa. Ya kuma bayyana taron a matsayin wata dama ta musamman ga masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinai ta sanayya tsakanin juna, don yin hulɗa tare da masu gudanarwa, baya ga hanyar sadarwa da zamantakewar da za ta shiga tsakanisu a taron na LIFACC 2024.
