Hukumar Hisba a Kano ta cafke matashin da ke neman sayar da kansa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta cafke matashin nan Aliyu mai shekaru 26 wanda yake neman mutumin da zai saye shi.

A ƙarshen makon jiya ne dai matashin ya riƙa yawo ɗauke da kwali da ya rubuta cewa shi na sayarwa ne duk mai buƙata ya biya Naira miliyan 20.

Da yake tabbatar da cafke matashin ga manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, babban Kwamandan hukumar ta Hisba Ustaz Muhammad Haroon Ibn Sina, ya ce, matashin ya aikata haramun.

Kazalika, ya ƙara da cewa hukumar ta kama Aliyu ne tun ranar Talata kuma ya kwana a hannun ta.

Gabanin cafkewar da hukumar ta yi masa dai, matashin ya ce, shi Tela ne kuma talauci ne ya addabe shi don haka ya yanke hukuncin sayar da kansa domin warware matsalar kuɗin da ya addabar shi.