Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gargaɗi al’ummar Musulmi da su guji ƙin yin azumin watan Ramadan da gangan.
A wani saƙon murya ta WhatsApp da ya aika wa manema labarai a Kano, kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Haroun Ibn-Sina, ya ce hukumar ba za ta ƙyale duk wanda aka samu yana cin abinci da rana ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
A cewarsa, hukumar Hisbah ba za ta naɗe hannunta tana ganin yadda matasa Musulmi ke keta hurumin addinin Musulunci a jihar ba, musamman a wannan wata mai alfarma, inda ake buqatar Musulmi su gudanar da cikakkiyar ibada ga Allah.
Haruna Ibn-Sina ya ƙara da cewa, hukumar Hisbah ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, wajen gudanar da aikinta na tabbatar da cikakken bin tsarin shari’ar Musulunci a cikin watan Ramadan da ma bayansa, inda ya ce duk wanda aka samu yana sava wa shari’a, za a hukunta shi.
Haruna Ibn-Sina ya jaddada cewa Hisbah ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yaƙi da baɗala a Kano.