Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna sun karɓi diyyar Naira miliyan 100 kafin sakin shugaban bankin kula da ayyukan noma a Nijeriya Alwan Hassan bayan ya kwashe kwanaki kusan 10 a hannunsu.
Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta ce saɓanin faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka gabatar cewar sun saki Hassan ne saboda yawan shekarun sa da kuma azumin watan Ramadan, wata majiya kusa da iyalan sa ta tabbatar da cewar sai da suka karɓi maƙudan kuɗi kafin sakin sa.
Jaridar ta ce ‘yan bindigar sun aike da saƙon bidiyo ga iyalan Manajan Bankin inda suka buƙaci a kai musu kuɗin ko kuma su hallaka shi, abinda ya sa iyalan suka kai musu kuɗin a wani dajin Jihar Kaduna, domin kubutar da shi.
Majiyar ta shaida wa jaridar cewar da farko an umurci iyalan da su kai kuɗin wani daji dake Jihar Katsina, amma kuma daga bisani sai aka ce musu su koma Jihar Kaduna, inda suka cimma tarin ‘yan bindigar ɗauke da makamai a wani daji, suka kuma miqa musu maƙudan kuɗin.
Faifan bidiyon da ‘yan bindigar suka gabatar na nuna cewar su ba su karɓi ko kwabo ba daga hannun manajan bankin kuma sun sake shi ne saboda yawan shekarunsa, inda suka buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta biya musu buƙatun su ko kuma su hallaka tarin fasinjojin dake hannun su yanzu haka.
‘Yan bindigar waɗanda suka rufe fuskokin su a bidiyon da suka gabatar ɗauke da manyan bindigogi, sun ce ita gwamnati ta san buƙatun su, saboda haka suna jiranta, kuma idan ta gaza za su hallaka fasinjojin da suka kama.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa a Nijeriya ta ce aƙalla fasinjoji sama da 140 ba a iya ganin su ba bayan ƙazamin harin da aka kai wa jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, yayin da wasu majiyoyi ke cewa waɗanda suka ɓata sun zarce wannan adadi ganin yawan mutanen dake neman ‘yan uwan su da suka ɓata.