Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) ta bayyana cewa ta karɓi Naira biliyan 15.17 daga Gwamnatin Tarayya tsakanin watan Janairu da Mayun shekarar 2026, yayin da ta ƙaddamar da manyan shirye-shiryen bunƙasa noma, lafiya, ilimi, ƙarfafa matasa da inganta tsaro a jihohi bakwai na yankin.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwar Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ne ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da rahoton ayyukan tsakiyar shekarar 2026 ga Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa maso Yamma.
Farfesa Ma’aji ya ce, a wannan lokaci hukumar ta fara fita daga matakin kafa tsarinta zuwa cikakken fara gudanar da ayyuka, inda aka samu ci gaba wajen shimfiɗa tsarin gudanarwa, tsara saye da kwangiloli, kulla haɗin gwiwa da kuma tsara manyan ayyukan raya yankin. Ya bayyana cewa, duk da an kafa hukumar ne ƙarƙashin Dokar Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa maso Yamma ta shekarar 2024, ba ta fara samun kuɗaɗen da doka ta tanadar mata ba sai a watan Janairun 2026.
A cewarsa, tsakanin Janairu da Mayu hukumar ta samu Naira biliyan 15.17, ta kashe Naira biliyan 1.2, yayin da har zuwa ranar 5 ga Yulin 2026 take da ragowar Naira biliyan 13.97 a asusunta. Ya ƙara da cewa, hukumar na ƙoƙarin samun ƙarin kuɗaɗe daga hanyoyin da doka ta tanada, ciki har da Asusun Tarayya, Asusun Muhalli da kuma kuɗaɗen harajin VAT domin aiwatar da ayyukan raya yankin.
Farfesa Ma’aji ya ce, gwamnatin jihar Kano ta bai wa hukumar ginin wucin gadi da take amfani da shi a matsayin hedikwata, yayin da gwamnatocin Kaduna da Katsina su ma suka bayar da gine-ginen da za a yi amfani da su a matsayin ofisoshin jihohi.
Haka kuma gwamnatin Kano ta bai wa hukumar motoci guda biyu da fili mai girman hekta biyu a Hotoro domin gina hedikwata ta dindindin, yayin da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi alƙawarin ba da ƙarin motocin aiki.
Bugu da ƙari, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bungudu/Maru, Abdulaziz Zubairu, ya bai wa hukumar kwamfutoci guda 20 da na’urorin bugawa guda biyar. Hukumar ta kuma ce tana shirin buɗe ofishin haɗin gwiwa a Abuja domin sauƙaƙa hulɗa da Ma’aikatar Tarayya ta Raya Yankuna, Majalisar Dokoki ta ƙasa da sauran hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Shugaban hukumar ya ce, an fara shirye-shiryen saye da aiwatar da ayyuka bisa ƙa’idojin gwamnati, bayan tattaunawa da gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma bakwai domin tantance abubuwan da suka fi buƙatar kulawa.
Daga cikin ayyukan da aka tsara akwai gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, gyaran makarantun sakandare, samar da tsaftataccen ruwan sha ta rijiyoyin burtsatse masu amfani da lantarki da hasken rana, sake tsugunar da ‘yan gudun hijira, horas da matasa kan sana’o’i da fasahar zamani, tallafa wa hukumomin tsaro da kuma bunƙasa harkokin noma.
Babban shirin da hukumar ta bayyana shi ne rabon taki kyauta ga gidajen manoma 30,000 a lokacin daminar shekarar 2026 domin ƙara yawan amfanin gona da inganta rayuwar al’ummar karkara.
Haka zalika, hukumar ta ƙaddamar da Shirin Horar da Matasa Sana’o’i, wanda zai bai wa matasa 10,000 horo kan sana’o’in hannu, fasahohin zamani da ilimin dijital ta cibiyoyi da ke Kano, Kaduna da Sakkwato. An kuma samar da wata manhajar rajista ta yanar gizo domin yin rajista da tantance masu cin gajiyar shirin. Domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro, hukumar ta ce tana shirin samar da motocin aiki da sauran kayan aiki ga hukumomin tsaro a faɗin yankin Arewa maso Yamma.
Farfesa Ma’aji ya kuma bayyana cewa hukumar ta fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin Kuwait, Saudiyya, Indiya da Rasha, waɗanda suka nuna shirinsu na haɗin gwiwa a fannoni kamar agajin jinƙai, ilimi, bunƙasa albarkatun ɗan Adam da ƙarfafa tattalin arziki.
Haka kuma ana ci gaba da tattaunawa da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Masu Hijira da Mutanen da Rikici ya Raba da Muhallansu (NCFRMI), ƙungiyar ADASHE Women Multipurpose Cooperative, eHealth Africa, Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) da UNESCO, kan shirye-shiryen samar da gidaje ga ‘yan gudun hijira, ilimin fasahar zamani, kiwon lafiya da tsara manyan tsare-tsaren raya yankin.
Har ila yau, hukumar ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a Kaduna domin tattara shawarwari daga masana wajen tsara babban shirin raya yankin na dogon lokaci.
Sai dai Farfesa Ma’aji ya shaida wa sanatocin cewa babban ƙalubalen da hukumar ke fuskanta shi ne jinkiri da ƙarancin kuɗaɗen da ake sakowa. Ya ce, duk da cewa an ware Naira biliyan 145.61 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin hukumar, abin da ake sakowa a kowane wata bai wuce kusan kashi uku cikin ɗari na abin da ake sa ran samu ba, lamarin da ke jinkirta aiwatar da ayyuka. Ya kuma ce bambancin fahimta tsakanin Kwamitin Gudanarwa da shugabannin gudanarwar hukumar game da fassarar dokar NWDC, tare da jinkirin gudanar da tarukan kwamitin, sun yi tasiri ga aiwatar da wasu shirye-shirye.
A ƙarshe, ya roƙi Kwamitin Majalisar Dattawa da ya taimaka wajen tabbatar da ana sakin kuɗaɗen kasafin hukumar cikin lokaci da kuma yadda ya dace da nauyin da doka ta ɗora mata. Ya kuma ƙara tabbatar wa ‘yan majalisar cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa gaskiya, riƙon amana da amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata yayin da take shirin fara cikakken aiwatar da ayyukanta a rabin na biyu na shekarar 2026.
