Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar tsara birane da
Jihar Katsina (URPB) ta fara tayar da waɗanda suka mamaye gefen hanyoyi da jikin bangayen gine-ginen gwamnati da sauran inda doka ta hana kasa kayan saye da sayarwa.
Wuraren da abun ya shafa sun haɗa da shatatalen High Court zuwa hanyar Daura da titin Sarki Abdulraman da kan kwanar High Court.
Sauran wuraren sune kan titin mai Shari’a Mohd Bello da na Isah Kaita kusa da gadar sama da ke GRA da wuraren da ake sana’o’i a jikin bangayen wasu ma’aikatu gami da jikin gadar sama da ke GRA nan cikin birnin Katsina.
Dukkan waɗanda aka tayar daga waɗannan wuraren, babu wanda ya nemi iznin hukumar, kafin zama a wuraren, domin a tsarin doka, sai an nemi izinin ko da zaman wucin gadi ne kamar yadda bayani ya fito daga hukumar.
Kuma kafin gudanar da wannan aiki sai da hukumar URPB ta bai wa mazauna wuraren takardar tashi (ejection notice), sannan aka tura jami’ai suka ƙara jaddada masu.
Wannan aiki na hana gudanar da wasu hidimomi, musamman kasa sana’o’i barkatai a haramtattun wurare, zai cigaba da gudana, domin tsabtacewa da kuma rage cunkoso a kan hanyoyi.
Janar manajan hukumar ta URPB TPL. Abbas Sambo ne, ya jagoranci wannan aiki, yace hukumar ta bai wa masu mazauna wuraren dama ta tsawon lokaci, tare da tunatar dasu illar abinda suka aikata ga dokar tsara birane, amman suka bijirewa hakan.
TPL. Abbas Sambo wanda ya yi roko ga al’umma da su din ga bin dokar tsara birane, yace akwai buƙatar mutane su dinga tuntuɓar hukumar kafin zama wani wuri, ko da zaman wucin gadi ne, domin hukumar kaɗai ke da alhakin amincewa ko akasin haka
Yace Gwamna Dikko Raɗɗa ya yi hanyoyi don inganta zirga-zirga don haka akwai buƙatar bin doka, don amfana da su, tare da jaddada yaƙinin yin aiki daidai da doka.
