ICPC ta tsare Ojerinde saboda badaƙalar milyan N900

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta cafke tsohon shugaban hukumar jarrabawar shiga jami’a (JAMB), Dibu Ojerinde bisa zargin badakalar Naira miliyan 900.

Jami’an hukumar ne suka cafke Ojerinde ran15 Maris a Abuja bisa zargin aikata zambar kuɗaɗe a lokacin da ya shugabanci hukumar JAMB da kuma Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO).

A cewar sanarwar da mai magana da yawun ICPC, Mrs. Azuka C. Ogugua
ta fitar, ana tsare da wanda ake zargin.

ICPC ta cafke Ojerinde bisa laifukan zambar kuɗaɗe ciki har odar sayo fensura da abun goge rubutu kan Naira miliyan 450 kowanne tsakanin 2013 da 2014.

ICPC ta nemi Ojerinde da amsa mata ‘yan tambayoyi kan bada bayanan karya, ƙin biyan haraji, fitar da kuɗin haram ketare da sauran su. Hukumar ta ce babu wata shaida da ke nuna inda kamfanoni biyu da Ojerinde ya bai wa kwangilar suke.

ICPC ta ce nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da Ojerinde gaban kotu.