Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Sumaila Kawu, ya bayyana cewa yana karɓar sama da Naira miliyan 21 a duk wata a matsayin jimillar kuɗin shiga gida.
Wannan fallasa dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta bayyana cewa kowane santana daga cikin sanatoci 109 da ke zauren majalisar na karɓar jimillar Naira miliyan 1.06 na albashi da alawus-alawus a kowane wata.
Shugaban RMAFC, Mohammed Shehu, ya bayyana hakan ne a matsayin ƙarin haske dangane da cece-kucen da ake tafkawa a baya-bayan nan kan adadin kuɗaɗen da kowane ɗan majalisa ke samu a wata.
Dangane da bayanin Shehu, hakan na nufin kowane ɗan majalisa yana samun Naira miliyan 21.72, wanda a cikin watanni 12 kum
