An nemi Kantoman Gaya ya fito takarar shugabancin ƙaramar hukumar

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yaba irin ayyukan raya ƙasa da shugaban riƙo na ƙaramar Hukumar Gaya, Hon. Abubakar Jazuli Gaya yake gudanarwa.

Irin gamsuwa da irin ayyukan da Kantoman riƙo na ƙaramar hukumar Gayan ne tasa jama’ar yankin ke son ganin ya amsa kiran tsayawa takarar neman shugabancin ƙaramar hukumar.

Wasu ‘yan siyasa suna nuni da cewa irin ayyukan da yake su ne irin ayyukan da tsarin Kwankwasiyya take so su ne irin wanda Gwamnatin Jihar Kano take.

Domin yana taimakon matasa da jari da taimakawa marasa lafiya da biyawa ɗalibai kuɗaɗen makaranta da gina makarantu har ma yana sa kuɗinsa ya gina makaranta.

Akan irin waɗannan ayyuka na kishin cigaban al’umma da Hon. Abubakar Jazuli Gaya yake a matsayin shugaban riƙon ƙaramar hukumar Gaya al’ummar yankin na da kyakkyawan fatan idan mutanen Gaya suka zaɓe shi ba za su yi da-na-sani ba, domin zai cigaba da irin waɗanan ayyuka na ci gaban al’umma da yake aiwatarwa.

By ukarofi