Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Gamayyar Jam’iyyu ta ƙasa reshen Jihar Kano wanda shine shugaban jam’iyyar ZLP na Jihar Kano da kuma ya yi wa jam’iyyar takarar Gwamna a zaɓen 2023, Alhaji Isah Nuhu ɗanfulani ya bayyana gamsuwa da tsare-tsaren hukumar zaɓe ta Jihar Kano na tunkarar zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin da suka kai ziyarar gani da ido da tattaunawa da shugaban hukumar zaɓen na Jihar Kano Sani Lawan.
Alhaji Nuhu Isah ɗanfulani ya ce sun tattauna bayanai gamsassu kuma shugaban hukumar ya ja hankalinsu akan idan sun tashi miƙa ‘yan takarkaru na jam’iyyu da za su yi takara su miƙa sunayen nagartattu tare da tabbatar musu za su yi adalci duk wanda jama’a suka zaɓa da yardar Allah za su tabbatar da shi.
ɗanfulani ya ce shi ɗan adam ba kwai ba ne da za a Kwankwaso shi, don haka yanzu za su zura ido su ga cewa ita hukumar zaɓen ta Jihar Kano za ta cika alƙawarin da ta yi kamar yadda ta ci alwashi ba a yayin da za a gudanar da zaɓen.
