Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris ta bayyana ƙudurinta na buɗe wata cibiya don sulhun ma’aurata a maimakon zuwa kotu kaitsaye.
Ta yi wannan bayani ne a wani taron da ƙungiya mai kula da sha’anin aure da ladubbansa, mai suna Aure Bautar Allah Women Multipurpose Cooperatiɓe Association Kebbi State.
Hajiya Zainab Nasare ta ce ba kowace matsala ce ya kamata a ce an je kotu kaitsaye ba ko a cikin gida ko unguwa ana ana iya sulhu.
Zuwa kotu tsakanin ma’aurata ba ƙaramar illa ya ke da ita ba musamman idan akwai yara tsakanin ma’auratan saboda a kotu akwai tonon asiri wanda a duniya ba wani sirri wanda ya kai na tsakanin mata da miji.
Akwai waɗansu matsaloli da rashin fahimta ne ke haddasa su wanda takaitaccen bayani ya Isa ya warware su ba tare da an shiga kotu ba.
Ta kuma nuna jin daɗinta bisa ga irin ayyukan da wannan ƙungiyar ke aiwatarwa a cikin jihar Kebbi musamman ta ɓangaren mata zawarawa da marayu.
“Na yi farin ciki matuƙa da wannan aikin jihadi da kuke yi kuma a shirye nake na bayar da nawa gudummuwa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso,” “inji ta.
Bayan kammala taron uwargidan Gwamnan Hajiya Zainab Nasare ta bayar da gudummuwar Naira Miliyan biyar tare da alƙawarin buɗe wata cibiya ta musamman wacce za ta rinƙa sulhun ma’aurata maimakon zuwa kotu kaitsaye nan ba da daɗewa ba in Sha Allahu.
Ta yi kira ga iyaye musamman mata da su cigaba da faɗakar da ‘ya’yansu mata da cewa fa shi aure fa ibada ne, duk wacce ta wayi gari a gidan miji ta sani fa ibada ta je yi domin neman tsira a gobe kiyama, a yi ladabi da biyayya ga Umar in mazaje muddin umarnin bai sabawa Allah ba sai ku zauna lafiya.
