Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Karl Toriola, Shugaban Kamfanin Sadarwa na MTN a Nijeriya, ya yi gargaɗin sosai game da mummunan halin da ɓangaren sadarwar Nijeriya ke ciki, yana mai bayyana shi a matsayin “tasku”.
Ya bayyna haka ne yayin wani jawabi da ya gabatar a wani taron zuba jari na kamfanonin sadarwa na zamani wanda Kamfanin Financial Deriɓatiɓes Company (FDC) ya shirya a ranar Talata a Legas.
Toriola ya jaddada buƙatar gaggawa na shiga tsakani don hana sashin rugujewa, yana mai nuni da cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, masana’antar za ta iya fuskantar ƙalubale masu tsanani da za su shafi masu kwastamomi.
Ya bayyana wajabcin gyare-gyaren farashin, wanda ya bayyana a matsayin “abin da ya zama dole” don ci gaba da ayyukan masana’antu.
Kalaman nasa sun sha banban sosai da kyakkyawan fata da Carl Cruz, shugaban kamfanin na Airtel Nigeria ya gabatar, wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa zuba jari za ta ci gaba da inganta fannin duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Toriola, ya jaddada cewa, ba tare da magance matsalolin da ke damun su ba, musamman ma buƙatar sake fasalin farashin, ɓangaren na iya fuskantar wani babban rikici.
