Indiya ta tabbatar da samuwar cutar Nipah

Spread the love

*Kasar ta bayyana sabbin mutane biyu masu ɗauke da cutar Nipah a West Bengal

Gwamnatin Indiya ta tabbatar da ɓullar sabbin cututtukan Nipah guda biyu a Jihar West Bengal da ke gabashin ƙasar, lamarin da ya janyo ƙarin tsauraran matakan binciken lafiyar matafiya a wasu ƙasashen kudu maso gabashin Asiya, musamman Thailand da Malaysia.

Ma’aikatar Lafiya ta Indiya ta bayyana hakan ne a ranar 28 ga Janairu, 2026, inda ta ce an gano cututtukan tun daga watan Disamba, kuma ana ci gaba da sanya ido sosai domin hana yaɗuwar cutar.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta gargadi jama’a da su kauce wa yaɗa jita-jita da alƙaluma marasa tushe, tana mai jaddada cewa adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a halin yanzu biyu ne kawai.

Hukumomin lafiya sun bayyana cewa mutane 196 da suka yi mu’amala da waɗanda suka kamu da cutar an riga an gano su tare da sanya su cikin tsauraran matakan sa ido.

A cewar hukumomi, dukkan waɗanda aka bi sawunsu ba su nuna wata alamar cuta ba. Gwaje-gwajen da aka yi musu sun nuna ba su ɗauke da kwayar cutar Nipah.

Wannan ya bai wa hukumomin damar cewa lamarin yana ƙarƙashin kulawa, wato sun tsagaita yaɗuwar cutar, duk da cewa ana ci gaba da taka-tsan-tsan.

A ɓangaren ƙasashen makwabta kuwa, Thailand ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar: Tsaurara binciken lafiyar matafiya da ke shigowa daga yankunan da aka samu ɓullar Nipah, ware wuri na musamman don ajiye jiragen sama daga yankunan da ke cikin hadarin kamuwa da cutar, tilasta matafiya cike takardun bayyana lafiyarsu kafin wucewa shige da fice.

Haka zalika, Malaysia ta bayyana cewa ta kara karfin shirye-shirye a dukkan tashoshin shigowa ƙasar, musamman kan matafiya daga ƙasashen da ke cikin hadarin ɓullar cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Malaysia ta ce tana cikin cikakken shiri da sa ido domin kare ƙasar daga yiwuwar shigar cutar ta iyakoki.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa cutar Nipah na daga cikin cututtuka mafi hadari a duniya, tana kuma da: Matsakaicin mutuwa tsakanin kashi 40% zuwa 75%. Babu rigakafi da ke hana kamuwa da ita. Babu magani na musamman da ke warkar da ita gaba ɗaya

Saboda haka, WHO ta sanya Nipah a jerin cututtukan da za su iya haifar da annoba ta duniya idan ba a daƙile su da wuri ba.

By ukarofi