Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR
Sunan fim: Balaraba
Kamfani: Mai Shadda Global Resources
Labari: Nura Hussaini
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo
Daukar Hoto: Moses Stephen/Saifullahi Deen
Sauti: Bello Minna
Daukar Nauyi: Abubakar Bashir Mai Shadda
Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda
M/ Umarni: Sadik Sani Sadik
Umarni: Abubakar Bashir Mai Shadda
Fim ɗin Balaraba, wani fim ne da ya bayyana rayuwar wani matashi Umar Faruk, mai tsananin fushi da hasala, ta yadda har ba ya iya yi wa harshensa linzami. Bai saurarawa kowa ba, abokai, dangi, kai har ma da mahaifinsa a wani takin. A tsaka da hakan ne auren shi ya ta so da wata mai suna Balaraba, wadda a yadda fim ɗin ya nuna ta fi fahimtarsa sama da kowa, wanda har dalilin hakan ya sa take tunasar da ‘yan uwanta cewar, “Ku kula, na rigada nasan halinsa, yanzu sai wani abin ya biyo baya.”
Amma fa duk da waccan kalar fahimta da amarya Balaraba ta yi wa Faruk, sai da aka kai ango karshe ya tsinka igiya guda ana kan hanyar kai mi shi ita gidansa.
Abubuwan burgewa:
A matakin farko na yabawa mai ba da umarni, watau Abubakar Bashir Mai Shadda. Duk da kasancewar wannan ne fim na farko da ya ba da umarni da kansa, matsayinsa na mai shirya fim ko ɗaukar nauyi, amma sai ya nunawa duniya cewar daidai, yana ba da wannan umarni. Ya cancantar da kowacce character, ta yadda ko ka ki ko ka so, sai ka ji a ranka waɗannan iyayen sun debo jini da yaran da aka sanya musu a matsayin diyan da suka haifa… kai har fa wani diban kama suke. A nan fagen Mai Shadda ka zamo karshe. Misali Radiya Jibril da aka sanyo ta a matsayin yayar amarya Balaraba, Asma’u Jika. Haka nan a ɓangaren waɗanda aka sanya a iyayensu ba a dauko uwa baka diya fara an saka ba.
Masu daukar hoto sun yi matuƙar ƙoƙarin da in ba ka yaba musu ba, a kai ka turu ko na yini guda ne. Sun yi amfani da saitin kalar hoton zamani, da jerantuwar kowacce gaba yayin tsaiwar jarumai a kamara.
A fita ma batun murya, kai da kake kallon fim ɗin kuma kake saurare, kai ka ce waɗanda ke maganar a kusa da kai suke ba cikin akwatin talabijin ba. Hakkina ne na yabawa mai daukar murya, da ku kanku sauran al’ummar gari da ke magana da Hausa.
A dan takaice, sauran ma’aikatan shirin (Crew’s) kuma ababen yabawa ne, an ba ku taurari na matakin ƙarshe.
Kura-kurai:
(1) Mun ga inda aka kawowa ango Faruk kayansa na sakawa amman sai ya nuna atafau ba a kyauta mi shi ba, nan ya fatattaki mai ɗinki. Can kuma sai aka fito harabar gidan abokin ango yana bai wa me ɗinki haƙuri. Ga abin mamaki sai muka ji me dinki na cewa, “Gaskiya ban ji dadi ba, duk yadda muka dade da shi amman yau ya min haka…” Ga mutumin da kuka dauki tsawon lokaci kuna huldar kasuwanci, ka rigada kasan asalin wane ne shi, don haka ba buƙatar sai ka sake gayawa wani kun jima amman ya yi maka haka, kuma abin ya dame ka. Ai bai ma kamata hakan ya dame ka ba. Sannan duk yadda ango ya kai ga lusaranci, ba yadda za a yi ya bar dinki sai ranar aurensa tukun a kawo mi shi kayan da zai saka don ya je ɗaurin aurensa. Ina ma laifin ace an kawo masa wasu amman na wurin wannan telan yake so ya saka amman shi ma ya bata masa.
(2) Can kuma sai muka ji uban amarya yana cewa “Ai ki na da lambata, saboda haka ki kira ni idan kin ga wani abu da ba ki gane ba…” Tuntuni amarya ba ta da lambar uban nata sai da aka zo tsaka da yi mata nasihar za ta bar gida zuwa gidan nata mijin? Sannan zai tuna cewar ko tana da lambarsa? Ina ma laifin ya ce, “Duk wani abu da ba ki gane masa ba ki kira ni.”
(3) Mutum mai irin halayyar Faruk ba ta yadda zai zama kamar wani dolo lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen daurin aure, don kawai abokansa sun ce yakamata ya saki fuskar shi. Scene din sai ya zama kamar wani wasan yara.
(4) Wajen ɗaurin aure, sai ya yi kamar ɗaurin ‘yar tsana. Yo to abokan ango da manyan mutane duk a tsaitsaye, sai ka ce ‘yan doka. Can kuma sai muka ji ana addu’ar daurin auren ita ma dai a tsaye, babu nuna wakilan ango, haka babu na amarya, uwa uba limami ma ya yi batan dabo. Mukaddara a cikin Masallaci aka ɗaura auren, amma ba a ganin yakamata a nuna waɗanda ke addu’a da sauran siga a cikin Masallacin? Ko a kofar gida a zaune kan tabarma?
(5) Mutumi da ke cikin irin wannan gida, ya girmewa mota, koda ma ace shi ba shi da ita, to yana da alfarmar motoci ba ma mota ba, musamman a irin wannan ranar da kowa ke son faranta masa. Amman sai muka ji ya ce abokin shi ya fita, ko ace makwabcinsa. Tun kan zuwan bikin ya ci ya nemo alfarmar motocin tunda ya nuna yana da dabi’ar za a soma kai amarya ba wai sai an zo ɗaukar ta daga gidan su ango ba.
(6) An saki amarya Balaraba, wadda kowa zai iya cewa laifin yayar ta ne domin ita ta yi musayar yawu da ango Faruk, amma sai muka ga kanwar mahaifiya na zaune, ba a nuna dattako na manya ba, wanda irin haka idan za ta faru suna dakatarwa, a matsayinsu na manya. Amman ta zamo hoto har aka kai ga yin sakin, duk kuwa da tun kafin a dauko amarya an nuna ba a shiri tsakanin yayar amarya da kuma kanwar mahaifiyar amarya.
(7) Fim fa ya sha talla ba karya. Kai ka ce don iya tallar aka shirya fim ɗin. Amman ko banza masu kallo za su san datar da ta dace su rika saya don wayoyin su.
Muna yabawa gami da fatan alkhairi.
