Daga MUKHTAR YAKUBU
Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Musa Maisana’a, ya yi wani taro na rabon buhuhunan dhinkafa da kuɗaɗe ga wasu daga cikin jaruman Kannywood da suke cikin buƙatar taimako ta ɓangaren buƙatun rayuwar yau da kullum.
Taron rabon kayan abinci da kuɗin wanda aka gudanar a ranar Litinin a cikin garin Kano ya samu halartar ɗimbin jama’a da suka halarci wajen domin samun rabon su na kuɗi da abinci da aka raba a wajen. A wajen taron dai an ga fuskokin tsofaffin jarumai masu yawa da suka halarci taron irin su Mallam Kabiru Nakwango, Isa Bello Ja, Jazuli Kazaza, Lubabatu Madaki da sauransu.
Da yake jawabi a game da rabon abinci da kuɗin tallafi ga ‘yan fim ɗin, Musa Misana’a ya ce “Ita wannan rayuwa yadda take, komai a wajen Allah yake, don haka komai sai da yardar sa ake yi. Don haka wannan abin da ka ga muna yi wani saƙo ne daga wajen Malam Nuhu Ribadu Mai ba shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro duba ga yadda ya ga ‘yan fim da ma duk wani da zai bada gudunmawa to a shirye yake da ya bada tallafi don a bai wa jama’a a matsayin gudunmawa domin ya ji dadin gudanar da rayuwarza cikin aminci. Kuma da buƙatar a wayar wa da mutane kai, a game da abin da ya shafi harkar tsaro, domin harkar tsaro ta kowa da kowa ce. Don haka duk wani da ya ga wani abu da zai cutar da al’umma to ya yi maza ya kai rahoton ga ofishin Nuhu Ribadu ya sanar. Ba kuma ana nufin a tafi Abuja ba don kai rahoton, a a ofishin ‘yan sanda mafi kusa da kai nan ne ofishin Nuhu Ribadu. Don haka duk wani da ya ga wani abu da zai cutar da al’umma zai hanzarta ya je ya sanar. Kuma za a bada gudunmawa yadda za a daƙile abin da zai cutar da al’umma nan take.
Wannan ya sa ake bayar da gudunmawa ga wanda ake ganin za su shiga gaba wajen wayar da kan al’umma, don haka wannan aikin ya shafi kowa da kowa ne har da kai domin a haɗu a wayar wa da mutane kai, wannan ba siyasa ba ce. Ko a cikin unguwarku, ko a kan hanya akwai waɗanda za ka samu suna wani abu na cutar da al’umma, kuma ana taron a zo a sanar da iyayen yaran ga matsalar yaransu ko a sanar da hukuma. To wannan ya sa al’umma suke ta cutuwa.
Dole ne sai al’umma sun fito, ko ɗanka ne ko ɗan wane idan ka ga zai cutar da al’umma ka fito ka wayar da kan al’umma a kan cewa wannan mai laifi ne, ko da ta ƙarƙashin ƙasa ne ka kai shi wajen hukuma, to ka taimaki jama’ar gari.”
Dangane da yadda aka tsara rabon ga ‘yan fim kuwa cewa ya yi ” Ai shi wannan rabon na kowa da kowa ne, su ‘yan fim da ka ga an fara da su, to su abokan gwagwarmaya ne kuma su ne idon da jama’a suke kallo, don haka muryoyinsu za su yi amo wajen kira ga jama’a da su sanar da hukuma idan sun ga wani abu da zai cutar da su. Kuma da yake kashi na farko ne da muka fara, a yanzu mun samar da tallafi na mutune hamsin, kowanne ya samu babban buhun shinkafa da Naira dubu hamsin. Kuma kamar yadda na faɗa wannan farko ne za a ci gaba da yi nan gaba. Muna fatan wannan abin ya ɗore a yi ta yi har tsawon rayuwar mu.
Domin mutane ba su san muhimmancin ciyarwa ba. Ko da mutum ba zai iya sayen buhun shinkafa ba idan ka sayi ruwa leda daya ka ajiye a kofar gidanka idan an dawo daga Masallaci duk wanda zai wuce ya ɗauka ya sha, to za ka ga sakamako.
Amma dai wannan da muke yi kuma za mu ci gaba da yi. Kuma daga ofishin Nuhu Ribadu ne kuma mun zaɓi mu bayar ga tsofaffin yan fim ne saboda a matsayin su na dattawa da waɗanda su ake kallo ake raga wa harkar kuma suna da ƙarfin faɗa a ji da za su wayar wa da mutane kai a game da harkokin tsaro da kuma muhimmancin zaman lafiya.”
