Sauya sheƙa: Gwamnoni ne jagororin APC a jihohinsu, inji Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dukkan gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar APC, sune jagororin jam’iyyar a jihohinsu, yana mai jaddada tsarin jam’iyyar yayin sauye-sauyen jam’iyyun siyasa.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron karɓar Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba zuwa APC da aka gudanar a Jalingo.

Shugaban ya yi wannan bayani ta bakin Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, inda ya ce bisa ga sauya sheƙar Gwamna Kefas daga PDP zuwa APC, ya zama jagoran jam’iyyar APC a Taraba.

Tinubu ya tabbatar da goyon bayansa ga gwamnan da gwamnatinsa domin kawo ci gaba a jihar.

Ya yaba da ƙoƙarin gwamnan wajen haɗa kan al’umma da daidaita bambance-bambancen da ke jihar, tare da kira ga al’ummar Taraba da su mara masa baya.

Shugaban ya kuma nuna farin ciki da samun gwamna daga yankin Arewa maso Gabas, yana kira ga Adamawa da Bauchi su shiga jam’iyyar APC.

A nasa jawabin, Gwamna Kefas ya ce sauya sheƙar ba don kansa ba ne, illa don makomar al’ummar Taraba, sannan burinsa shine samar da ayyukan yi, tallafa wa ’yan kasuwa, da kawar da rarrabuwar kai, talauci da rashin tsaro acikin al’umma.

By Babaji