INEC ta tabbatar da cikakken biyayya ga sharuɗɗa yayin da jam’iyyu 22 za su fafata a zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa guda 22 da aka yi wa rajista a Nijeriya sun cika sharuɗɗan doka ta hanyar miƙa kundin rajistar mambobinsu kafin wa’adin da aka ƙara musu.

A wata sanarwa da INEC ta fitar, ta bayyana cewa jam’iyyun sun kammala aikin ne kwanaki biyu kafin sabon wa’adin ranar 10 ga Mayu, 2026 da ta bayar ya cika.

Da fari hukumar ta sanya 21 ga Afrilu, 2026 a matsayin ranar ƙarshe domin miƙa mata kundin mambobi daga ɓangaren jam’iyyun kamar yadda yake cikin jadawalin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Daga bisani bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyun a ranar 24 ga Maris, 2026, INEC ta amince da ƙara wa’adin da makonni biyu, wanda ya ba kowace damar kammala aiki a kai gabanin cikar wa’adin.

INEC ta ce, an ɗauki matakin ne domin ba su damar tsara zaɓukan fidda gwani yadda ya dace, musamman ganin cewa jam’iyyun sun gabatar da sababbin ranakun gudanar da zaɓensu na cikin gida.

Wannan tsari ya yi daidai da Sashe na 77(4) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi cewa wajibi ne jam’iyyun siyasa su miƙa kundin rajistar mambobinsu aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fidda gwani.

By Babaji