INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai tsaye

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta ce tana shirin ƙaddamar da wata na’ura da za ta ba ta damar bibiyar shirye-shiryen babban zaɓen 2027 kai tsaye daga kowace jiha.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas, yayin wani taron bita na musamman da aka shirya wa sakatarorin gudanarwar hukumar.

Ya ce taron bitar na da nufin samar da ingantacciyar na’urar bibiyar ayyuka ta amfani da Eɗcel, wadda za a haɗa da dandamalin intanet na Cibiyar Sa-Ido da Taimakon Zaɓe ta INEC da kuma Tsarin Ayyukan Zaɓe.

Amupitan ya ce a baya hukumar ba ta da wani tsari guda ɗaya da zai ba ta damar bibiyar ayyukan da ke gaban sakatarorin gudanarwar INEC a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa sabuwar na’urar za ta ba kwamishinonin zaɓe na jihohi, manyan jami’an sa-ido, sakataren hukumar da kuma hedikwatar INEC damar samun bayanai nan take kan yadda shirye-shiryen zaɓe ke gudana.

A cewarsa, bayanan za su haɗa da rarraba kayayyakin zaɓe, horar da ma’aikatan wucin-gadi da kuma matakin shirye-shiryen zaɓe a kowace jiha.

“Wannan zai ba mu damar sauyawa daga mayar da martani ga matsaloli bayan sun faru, zuwa tsarin gudanarwa mai hangen nesa da ɗaukar mataki tun kafin matsala ta taso,” inji shi.

Shugaban INEC ya ce matakin ya zama dole musamman ganin cewa adadin masu rajista a rajistar masu zaɓe ta ƙasa na dab da kai wa miliyan 100.

Ya ƙara da cewa taron bitar zai tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi ci gaba da rajistar masu zaɓe, sufuri da sarrafa kayayyakin zaɓe, amfani da fasahar zaɓe, inganta ayyukan ma’aikatan wucin-gadi da kuma bin ƙa’idojin kuɗi.

Amupitan ya ce hukumar za ta yi amfani da nasarori da darussan da ta koya daga zaɓukan da aka gudanar a wasu jihohi wajen inganta shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Ya ce INEC na fatan tabbatar da cewa nasarorin da aka samu a waɗancan zaɓukan za su zama ginshiƙin inganta tsarin zaɓe a faɗin ƙasar yayin babban zaɓen 2027.

By ukarofi