
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Iran na duba yiwuwar ficewa daga gasar cin kofin duniya na 2026 a hukumance.
Hakan na nufin tawagar ‘yan wasanta ba za su je ƙasar Amurka ba domin fafatawa a wasannin gasar ba na wannan shekarar.
A sabon jaddawalin wasannin, Iran na da uku na rukuni da za ta yi da wasu ƙasashe a Amurka.
Iran ta yi imanin cewa rayuwa ba za a iya kwatanta ta da ƙwallon ƙafa ba kuma ba za ta ɗauki haɗarin zuwa gasar cin kofin duniya ba.
A halin yanzu an shiga kwana na biyu ana fafata yaƙi tsakanin ƙasar da Amurka da Isra’ila, wanda ya yi sanadin mutuwar jagoran Musuluncin Iran.
