
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta shawarci ’yan Nijeriya mazauna Gabas ta Tsakiya musamman ma Iran da ƙasashen yankin Gulf, da su ƙara ɗaukar matakan tsaro sakamakon tashin hankali a yankin.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a ranar Asabar, gwamnati ta ce tana sa ido kan rahotannin hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin Iran da ya shafi sassan yankin Gulf.
Hukumomi sun buƙaci ’yan Nijeriyar da su kasance a faɗake, su guji wuraren da ake kai wa hari kamar sansanonin soji da gine-ginen gwamnati.
A sanarwar, Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya bayyana cewa ma’aikatar ta fitar da wasu shawarwari guda biyar kamar haka: Gwamnati ta shawarci ‘yan Nijeriya da su guji zirga-zirga a kusa da sansanonin soji, gine-ginen gwamnati, ko wuraren da ake ganin za su iya zama matattarar rikici; an bukaci mutane da su zauna a gida muddin ba wata muhimmiyar bukata ce ta fitar da su ba, sannan su guji shiga taron jama’a ko zanga-zanga; ‘yan kasa da su kiyaye dukkan dokoki da matakan tsaro da hukumomin kasashen da suke ciki suka gindaya; Ma’aikatar ta bukaci mutane da su rinka sauraron kafafen yaɗa labarai na ƙasa-da-ƙasa masu gaskiya, sannan su kiyayi yaɗa labaran bogi.
A ƙarshe, sanarwar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke Tehran (Iran), Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudi Arabiya suna cikin shirin ko-ta-kwana don tallafa wa duk wani dan Nijeriya da ya shiga cikin matsala.
Har ila yau, Gwamnatin Nijeriyar ta kirayi ɗaukacin ɓangarorin da rikicin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su ajiye makamai su koma kan teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya a duniya.
