Mutum huɗu sun mutu wajen rabon sadakar azumi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Lamarin ya faru ne a gidan wani attajiri, Alhaji Dahiru Usman Sarki a unguwar ƙofar Guga da ke cikin garin Katsina.

Bayani ya nuna cewa a duk shekara idan an fara azumin watan Ramadan ya kan raba sadakar kuɗi ga mabuƙata.

Dubban mutane da suka haɗa da maza,mata,yara da masu buƙata na musamman suke cincirindon a unguwar domin karɓar sadakar kuɗi da attajirin ke badawa a duk shekara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Ya bayyana cewa tirmitsitsi da ya faru sakamakon yawan mutane da suka je gidan attajiri karɓar sadaka ya jawo rasuwar mutane huɗu wasu kuma sun sami raunuka.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa yanzu haka yan sanda na binciken faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ‘yan sanda a jihar tana shawarar duk masu bada irin wannan sadaka da su tuntuɓi yan sanda domin bada kyakkyawan tsaro a wurin bada sadakan.

Irin wannan ta taɓa faruwa a shekarun baya gidan wani attajiri a cikin garin Katsina inda aka rasa rayuka.

By ukarofi